Wani jami’in Amurka ne da ba a bayyana sunan shi ba, ya tabbatar wa jaridar Wall Street Journal cewa bayanan sirrin Amurka sun taimakawa Faransa kashe Mokhtar Belmokhtar mai ido guda.
Labarin kisan Kwamandan na Al Qaeda a Afrika na zuwa a yayin da ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian ke shirin tattaunawa da takwaransa na Amurka Ash Carter.
Labarin kashe Belmokhtar dai ya zama abin taka-tsantsan, ganin sau da yawa an sha ikirarin kashe shi amma daga baya sai ya sake bayyana da rai.288